Mutane na zanga-zanga a Ouagadougou

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Campaore ya shafe fiye da shekaru 26 a kan mulki

Dubban mutane sun bazama kan tituna a Ouagadougou babban birnin Burkina Faso, kan batun gyaran kundin tsarin mulkin kasar.

Mutanen na yin zanga-zangar ce domin kin amincewa da kokarin bai wa shugaban Burkina Faso Blaise Compore damar yin wani wa'adi na shekaru biyar a kan mulki.

An rufe makarantu ciki har da jami'o'i domin gudun tashin hankali a kasar.

Mr Compaoré na kan mulki tun a shekarar 1987 lokacin da ya yi juyin mulkin soji a kasar.