'Yan tawaye sun sace mutane 5 a Kamaru

'Yan tawayen Seleka Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan tawayen na neman Kamaru ta saki madugunsu, Abdoullahi Miskine

Rahotanni daga jamhuriyyar Kamaru na cewa, an sake yin garkuwa da wasu mutane biyar a yankin gabashin kasar.

Mutanen da aka yi garkuwar da su a Garoua-Boulai mai iyaka da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, sun hada da wani basaraken gargajiya da wasu direbobin manyan motoci.

Bayanai na nuna cewa an shigar da mutanen da aka sacen cikin Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

A 'yan watannin baya-bayan nan ne ake zargin wata kungiyar 'yan tawaye mai alaka da kungiyar Seleka da kara kaimi wajen garkuwa da mutane da kuma kai hari a Kamaru.

Karin bayani