An cike gibi tsakanin Maza da Mata a duniya

Kungiyar tattalin arziki ta duniya ta ce a cikin shekara guda an ci gaba da tsuke gibin da ke tsakanin maza da mata sakamakon shigar da mata suke yi cikin siyasa da harkokin tattalin arziki.

A wani rahoto da ta fitar, kungiyar ta yi nazari kan abubuwa irinsu tattalin arziki da kiwon lafiya Da ilimi da yadda ake shiga siyasa a kasashen 142.

Tun lokacin da ta fara fitar da rahoto kan wannan batu shekaru tara da suka gabata, kungiyar ta ce kasashe 105 sun rufe gibin da tsakanin maza da mata, sai dai duk da haka akwai gubi guda biyar da ke da matukar tayar da hankali.

Iceland ta ci gaba da kasancewa jagaba a kan rufe gibi tsakanin maza da mata sau shida a jere, yayin da kasar Yemen ta kasance kurar-baya.

Sauran kashe da ke biye wa Iceland su ne Finland da Norway da Sweden.

Tun tuni kasashen suka yi bukukuwan murnar ci gaban siyasa da suka samu.

Burtaniya ta fadi kasa da maki takwas a cikin kasashen da ke tsuke gibin da ke tsakanin maza da mata inda a yanzu take ta 26, yayin da Rwanda ta tagaza zuwa matsayi bakwai a bayan kasashe 20 da suka yi zarra kan wannan batu, lamarin da ya sanya ta kasance kasar Africa ta fi karfin tattalin arziki.

Kungiyar tattalin arziki ta duniyar ta ce sauyin da aka samu game da hanyoyin samun kudin mata shi ne ya sanya Burtaniya ta gaza.

A bangare guda kuma, Amurka ta zuwa matsayi na 20 saboda gibin da ake da shi na samun kudi a kasar ya ragu, sannan adadin matan da ka zaba zuwa majalisun dokoki da wadanda aka nada a matsayin ministoci ya karu.

Matar da ta wallafa wannan rahoto, Saadia Zahidi ta ce Rwanda ta yi nasara ne saboda adadin matan da ke aiki ya kusa kai wa na maza, sannan an nada mata da yawa a matsayin ministoci; ba wai ta samu nasara ba ne saboda inganta kiwon lafiya da ilimi.

Wani abin mamaki kuma shi ne yadda kasar Nicaragua, wacce ta matsa zuwa mataki na shida daga na goma, ta kasance kasar nahiyar Asia da ta fi bai wa mata dama, fiye da Philippines.

An yi la'akari da matakai hudu domin ganin kasasr da ta fi bai wa mata dama.

· Shin mata suna iya yin aiki, kuma ana ba su irin damar da aka bai wa maza?

· Shin ana bai wa mata ilimin da ya dace?

· Shin ana barin su su shiga harkokin siyasa?

· Shin ana kula da kiwon lafiyarsu/ A kawai ana duba kiwon lafiyar ba, shin ya ya rayuwarsu take idan aka kwatanta su da maza?

An samu yawancin wannan sakamako ne bisa yin la'akari da harkokin yau-da-kullum.

Alal misali, kasar India ta gaza daga mataki na 13 zuwa na 114 a wannan shekarar, kuma ita cekurar-baya a cikin kasashen Brics .

Ms Zahidi ta ce mata ba sa shiga harkokin al'umma a India saboda tambayar da suke yi cewa ba a tsaron lafiyarsu idan suka shiga motocin hanya.

Ta kara da cewa an cike gibi tsakanin maza da mata ne musamman saboda shigar mata cikin harkokin siyasa da ayyukan yi.

Rahoton ya kara da cewa: "kodayake maza da mata sun hada gwiwa a cikin sheakru goma da suka gabata, amma a kasashe 49 an fi samun matan da suka je neman ayyuakan yi fiye da maza.

Ya ce: "haka kuma a harkokin siyasa ta duniya gaba daya, an samu karin kashi 26 na matan da aka zaba a majalisun dokoki, sannan aka samu kashi 50 ciki 100 na matan da aka bai wa mukaman ministoci fiye da yadda yake a shekaru goma da suka wuce."

Ms Zahidi ta ce kasashen sun samu tagomashi ne saboda wa'adin da aka dibar musu da kuma kayyade iya matan da ake so a bai wa mukamai na siyasa.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service