Dalibai sun yi zanga-zanga a Kaduna

Nigeria
Image caption Yin zanga zanga a a Jami'o'in Nijeriya ba sabon abu ba ne

A jahar Kadunan Nijeriya wasu dalibai masu koyon aikin likita na jami'ar jahar sun gudanar da wata zanga-zanga domin nuna damuwa bisa halin da suke ciki.

Daliban wadanda suka kange kofar shiga jami'ar, na kokawa ne bisa rashin ci gaba da 'yan uwansu da suka shiga aji uku na koyon aikin likita ke fuskanta.

Hakan a cewarsu ya biyo bayan rashin tantance makarantar daga gwamnatin tarayya.

Baya ga haka, akwai korafin rashin kammala ayyuka a asibitin koyarwa na jami'ar da rashin biyansu wadansu alawus - alawus da suka kamata a cewar daliban.

A kokarin warware irin wannan matsala ne a baya gwamnatin ta kai wasu daga cikin daliban jami'ar Kampala dake kasar Uganda, domin ci gaba da karatun na su.

To sai dai duk da haka daliban sun ce basu gamsu da wannan yunkuri ba.