PDP ta nemi Tambuwal yayi murabus

Tambuwal Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kakakin Majalisr wakilai a Nigeria

Jam'iyyar PDP mai mulki a Nigeria ta yi kira ga kakakin majalisar wakilai, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal da ya sauka daga kan mukaminsa bayan da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta APC

Jam'iyyar PDP ta ce kwamitinta na gudanar da aikace-aikace, watau National Working Committee ya gana da shugabannin jam'iyyar a majalisar wakilai akan sauya shekar ta kakakin majalisar, kuma bayan ta yi nazari akan al'amarin ta bukaci kakakin da ya nuna dattako tun da sabuwar jam'iyyarsa ita ce maras rinjaye a majalisar.

A cikin wata sanarwa da sakataren watsa labarai na jam'iyyar ya fitar, Jam'iyyar ta ce kamata yayi Kakakin Majalisar a matsayin zababben jami'i mai dattako, ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa tun da ya fice daga cikin jam'iyya mai rinjaye a majalisar wakilan.