Tambuwal ya koma APC

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Tambuwal tare da tsohon shugaban majalisar wakilai, Aminu Masari

Bayan jan kafa na wani lokaci, shugaban majalisar wakilan Nigeria, Aminu Tambuwal ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP mai mulki zuwa jam'iyyar adawa ta APC.

A ranar Talata, Tambuwal ya sanarda matsayinsa a zauren majalisar a Abuja.

Matakin ya kawo karshen lokaci mai tsawo da ake zargin cewar shugaban majalisar zai bar PDP ya koma APC saboda ya tsaya takarar gwamna a jihar Sokoto.

Jim kadan bayan da Tambuwal ya sanarda sauya shekar sai ya dage zaman majalisar zuwa ranar 3 ga watan Disamba.

A makon da ya gabata ne, Tambuwal ya halarci taron 'yan jam'iyyar APC a Sokoto amma kuma ya ce bai sauya sheka ba.