Ba zan fice daga APC ba - Atiku

Image caption Atiku zai fuskanci kalubale daga Buhari da kuma Kwankwaso

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Atiku Abubakar ya ce ba zai fice daga jam'iyyar APC ba duk yadda zaben fitar da gwani na shugaban kasa ya kasance.

Sanarwar da ofishin hudda da jama'a na Atiku suka fitar, ta ce ba zai sauya sheka zuwa jam'iyyar PDM ba ko da jam'iyyar APC ba ta tsayar da shi takara ba a zaben 2015.

Sanarwar ta ce rahoton wata jarida kan batun cewar Atiku zai iya barin APC ba gaskiya bane.

Kawo yanzu mutane hudu ne suka yi shelar tsayawa takarar shugabancin Nigeria a jam'iyyar APC, watau Janar Muhammadu Buhari da Gwamna Rabiu Kwankwaso da Atiku Abubakar da kuma Sam Nda Isaiah.

Akwai rarrabuwa kawuna tsakanin 'ya'yan jam'iyyar APC kan tsarin da yafi dacewa a bi wajen tsayar da dan takarar jam'iyyar a zaben 2015.