Boko Haram ta kutsa garin Uba

Yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto AFP

Rahotanni daga yankin arewa maso gabashin Nigeria na cewa 'yan kungiyar Boko Haram sun afka wa garin Uba.

Garin na Uba a karamar hukumar Uba Askira yana tsakanin Jihar Borno ne da Adamawa, kuma tuni jama'a da dama sun fice daga garin.

Kawo yanzu babu cikakken bayani a kan yawan mutanen da suka jikkata, amma wasu rahotanni sun ce tun a daren ranar Talata ne aka yi ta jin karar fashe-fashen abubuwa a garin Uba.

Bayan kama garin na Uba inda aka ce sun kafa tuta, wasu rahotannin sun ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun doshi Mararbar Mubi.

Ko da yake basu kai ga isa garin Mubin ba, amma wasu mazauna garin sun ce a yanzu haka jama'a na gudu daga garin.

Wani mazauna garin ya shaida wa BBC cewa ya ga mutane da dama suna ta gudu ciki har da jami'an tsaro a keke Napep.