'Yan Boko Haram sun durfafi garin Mubi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko Haram ne ke da iko a garuruwa da dama a Borno da Adamawa

Rahotanni a Nigeria na cewa 'yan Boko Haram sun durfafi garin Mubi da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar.

Hakan na faruwa ne, duk kuwa da sanarwar yarjejeniyar dakatar da bude wuta da gwamnatin kasar ta ce ta cimma da 'yan Boko Haram.

Garin na Mubi wanda ke kusa da iyaka da kamaru shi ne gari na biyu mafi girma a jihar Adamawan.

Wani dan garin ya sheda wa BBC cewa jama'a sun firgita suna barin garin.

Tun da farko an bayar da rahotannin cewa 'yan Boko Haram din sun kama garin Uba na jihar Borno.

Tun daga watan Yulin bana, 'yan Boko Haram ke ci gaba da kwace iko a garuruwan da ke arewa maso gabashin Nigeria.