An rage saurin yaduwar Ebola a Liberia

liberia ebola Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce mai yiwuwa an sami ragi a saurin da cutar Ebola ke bazuwa a Liberia - amma ta yi gargadin cewa zai zama azarbabi idan aka ce an shawo kanta ke nan.

Mataimakin Babban Magatakardan Hukumar, Bruce Aylward, ya sheda ma taron manema labarai cewa karuwar da ake samu ta tsaya a kan adadi guda.

Mr Aylward ya ce,akwai dalilai da ake ganin su suka haddasa hakan.

Ya ce, ''A tuna cewa Liberia ta dade tana fama da wannan cuta zuwa yanzu.

Akwai gagarumin kokarin fadakar da jama'a a kan cutar, domin su sauya dabi'un da ke jefa su cikin hadarin kamuwa da ita.''

Sai dai kuma, Mataimakin Babban Magatakardan na Hukumar Lafiya ta Duniya, ya ce kwararru na gudanar da bincike akan alkaluman, yana gargadin cewa 'yar raguwar da ake gani ba tana nufin an dakile annobar ta Ebola ba ke nan.