Ana kazamin fada a garin Mubi na Adamawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kawo yanzu babu cikakkun bayanai ko 'yan Boko Haram sun kwace garin Mubi

Rahotanni daga garin Mubi na jihar Adamawa sun nuna cewar ana kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati da mayakan Boko Haram.

Mazauna garin sun ce sun ji karar harbe-harbe sannan kuma jiragen yaki na soji na shawagi a garin.

Bayanai sun ce dubban mutane na fice wa daga garin domin tsira da ransu.

Garin na Mubi wanda ke kusa da iyaka da Kamaru shi ne gari na biyu mafi girma a jihar Adamawa.

A farkon watan nan, gwamnatin Nigeria ta sanar da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da 'yan Boko Haram, abin da zai kai ga sakin 'yan matan Chibok su sama da 200 da 'yan Boko Haram din suka sace sama da watanni shida.