Shugaban kasar Zambia ya mutu

Zambia Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Michael Sata ya karbi mulkin Zambia ne a shekarar 2011 bayan da ya lashe zabe a karkashin jam'iyar Patriotic Front

Shugaban kasar Zambia, Michael Sata ya mutu a wani asibiti da ke birnin London yana da shekaru 77 a duniya.

Sakataren majalisar ministocin kasar, Dr Roland Msiska ne ya sanar da mutuwar shugaban kasar a ranar Laraba.

Marigayin ya kwashe watanni yana fama da rashin lafiya, ko da yake ba a bayyana ciwon da ya yi ajalin nasa ba.

Mutuwar tasa ta zo ne 'yan kwanaki bayan kasar ta yi bukukuwan cikarta shekaru 50 da samun 'yancin kai.

Kawo yanzu babu tabbacin wanda zai maye gurbinsa, ko da yake ministan tasro na kasar Edgar Lungu ne ya zamo mukaddashin shugaban kasar bayan Mr. Sata ya fita kasar waje jinya.