Argos na fuskantar matsalar Internet

Shafin Internet
Image caption Shafin Internet

Kamfanin nan mai sayar da kayayyaki Argos ya fuskanci matsaloli a rana ta biyu bayan sake sabuntawa da zayyanar shafinsa na internet.

Yana nuna wani sako na kuskure ga wasu komputoci amma banda wasu, kuma sakon yana nuna cewar an toshe hanyar shiga shafin saboda masu ziyarar sa sun yi yawa.

Masu shiga shafin dai sun yi koken cewa wannan ba daidai ba ne, saboda irin yadda ake nuna sakon tun da sanyin safiya kuma batun na cigaba.

Kamfanin na Argos ya ce wannan wata matsala ce da ake yawan samu, za a kuma iya daukar wani lokaci mai tsawo kafin a shawo kan ta.

Kamfanin wanda mallakar rukunin kamfanonin nan ne na Milton-Keynes ya ce shafinsa yana aiki a yanzu haka to amma za a iya fuskantar wasu matsaloli na shiga cikinsa.

Wata mai magana da yawun kamfanin ta sheida ma BBC cewar, "sakamakon gyaran shafin na Internet da apps, suna cigaba da fuskantar matsaloli wanda ke nufin masu hudda da kamfanin za su iya samun shiga shafin a wasu lokutta, amma kuma a wasu lokuttan ba za su samu shiga ba."

"Ta nemi afuwa ga matsalolin da mutane ke fuskanta. Tace, tarbar abokan huddarmu hannu bibbiyu shine abinda muka baiwa fifiko, muna kuma kokarin warware wannan matsalar nan ba da jimawa ba."

Tace, ranar talata ne kawai wani dan lokaci aka toshe kafar shiga shafin ga kowa-da-kowa.

Kamfanin ya yi amfani da hanyar sada zumunta ta zamani don neman afuwa saboda wannan matsalar, to amma sai abokan abokan huddar kamfanin da suka nemi ganin wannan sako ne za su iya ganin sa.

Mai magana da yawun kamfanin tace, "rashin fitowar dalilan da suka sa ake samun matsalar a shafi ita kan ta, wani batu ne na fasaha wanda a yanzu haka ake kokarin magancewa.

Karin bayani