'Yan Boko Haram sun shiga garin Vimtim'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Garin Vimtim ba shi da nisa da garin Mubi

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun shiga garin Vimtim.

Maharan sun shiga mahaifar babban hafsan sojin Najeriya, Air Marshal Alex Badeh ne a ranar Alhamis.

Tsohon shugaban karamar Hukumar Mubi ta arewa, John Kwale Vimtim ya tabbatar wa da BBC hakan.

Ya kara da cewa da shiga garin na Vimtim, maharan suka nufi gidan babban hafsan sojin Najeriyar kai tsaye.

Sai dai babu wanda suka kashe saboda mutanen garin baki daya sun tsere bayan samun labarin karbe garin Mubi da 'yan Boko haram din suka yi a ranar Laraba.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba