An kafa dokar ta-baci a Burkina Fasso

Hakkin mallakar hoto ap

Babban hafsan sojin Burkina Fasso, Janar Honore Traore ya bayyana rushe gwamnati da majalisar dokoki ta kasar da kuma cewa za a kafa wata gwamnatin wucin gadi , da zata tuntubi dukkan jam'iyyun siyasar kasar.

Shi ma Shugaban kasar, Blaise Compaore, ya sanar da rushe majalisar ministoci, kana ya ce zai fara tattaunawa da 'yan adawa.

Mr Compaore ya kuma kafa dokar ta-baci, tare da yin kira ga 'yan adawa da su kawo karshen zanga-zangar.

Tashin hankali ya barke a birnin Ouagadougou , inda masu zanga-zangar suka bankawa majalisar dokoki wuta, domin nuna rashin amincewarsu da tsawaita wa'adin mulkin Mr Campaore na shekaru ashirin da bakwai.