Abbas ya yi martani kan rufe Masallacin Kudus

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Bayahuden na kwance rai kwa-kwai mutu kwa-kwai

Shugaban Falasdinawa, Mahmoud Abbas, ya bayyana rufe harabar Masallacin Al-Aqsa da Isra'ila ta yi a matsayin kaddamar da yaki.

'Yan sandan Isra'ila sun rufe harabar ne bayan harbin wani Bayahude mai tsananin ra'ayin rikau, Rabbi Yehuda Blick da aka yi a ranar Laraba.

'Yan sandan Isra'ilar sun harbe wani Bafalasdine, wanda suka zarga da harbin Yehuda Blick a gaban wani dakin taro.

Bayahuden na magana ne kan bai wa karin yahudawa damar shiga masallacin a lokacin da aka kai masa harin.