An gurfanar da mace kan kashe mijinta a Kano

Kotu ta sanya ranar 26 da 27 ga watan Nuwamba domin fara sauraron shedu

Asalin hoton, BBC World Service

Bayanan hoto,

Kotu ta sanya ranar 26 da 27 ga watan Nuwamba domin fara sauraron shedu

A jihar Kano da ke arewacin Nigeria, an gurfanar da matashiyar nan da ake zargi da kashe mijinta da wasu mutane uku ta hanyar zuba guba a abincin mijin.

An gurfanar da Wasila Umar mai shekaru 14 ne a gaban wata babbar kotun jihar da ke garin Gezawa, inda aka tuhume ta da aikata laifin.

Sai dai lokacin da aka karanta mata tuhumar, matashiyar taki cewa komai, abin da yasa kotun ta dauki shurun nata a matsayin rashin amincewa da tuhume-tuhumen da ake yi mata.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da na mata na daga cikin wadanda suka halarci zaman kotun.

Idan har an samu Wasila da laifi, za ta iya fuskantar hukuncin kisa karkashin kundin shari'a na jihar Kano.