Sarkin Kano ya ziyarci Shugaba Jonathan

Hakkin mallakar hoto state house
Image caption Sarki Muhammadu Sanusi ya ziyarci Mr Jonathan sau biyu tun bayan darewa karagar mulki

Bayan shafe lokaci suna zaman doya da manja, Shugaba Goodluck Jonathan da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II sun gana a fadar Aso Rock.

Hakan ya biyo bayan ziyarar da Sarkin Kano ya kai wa Mr Jonathan a fadarsa da ke Abuja ne a ranar Alhamis.

A cikin watan Fabarairu, Mr Jonathan ya kori Sarki Sanusi daga mukamin gwamnan babban bankin Nigeria bayan ya yi zargin cewar an yi sama da fadi da fiye da dala biliyan 20 na harajin danyen mai.

A watan Yuni, bayan rasuwar Sarki Ado Bayero, sai gwamna Rabiu Kwankwaso ya nada Sarki Sanusi a matsayin sarkin Kano.

Bayan nadin Sarkin Kano sai da aka shafe mako guda bai shiga fadarsa ba yana gidan gwamnatin jihar Kano bisa fargabar cewar jami'an tsaro za su kama shi.