2015: Jonathan ya karbi fom din takara

Shugaba Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya sayi fom din tsaya wa takarar sake shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP.

Hakan ya sa yanzu ta tabbata cewa zai sake neman wani wa'adin mulki ba tare da hamayya a jam'iyyarsa ta PDP ba.

Dr. Abubakar Kari masanin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja, ya bayyana cewa dama dukkan alamu sun nuna Jonathan din zai fito takara.

Dr Karin na ganin watakila tunanin kalubalantarsa karkashin tsarin mulki ne dama ya hana shi ambaton zai yi takarar.

Karin bayani