'Yan bindiga sun kashe sojojin Nijar tara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Inda aka kai hare-haren na da iyaka da kasar Mali a cikin jihar Tillaberi

Rahotanni daga yankin arewa-maso-yammacin Nijar na cewa wasu mahara da ake zargin mayakan Mujao ne sun kai hari yankin inda suka kashe sojojin Nijar tara.

Maharan da ake zargin sun fito ne daga Mali sun kuma raunata wasu karin sojoji biyar a lokacin harin.

Wakilin BBC da ya ziyarci yankunan ya ce maharan sun kai hare-hare uku ne a lokaci guda da asubahin ranar Alhamis.

An dai kashe sojoji hudu a sansanin 'yan gudun hijirar 'yan Mali da ke Mangaize, sannan an kuma kashe wasu sojojin biyar a Zarumda rai.

'Yan bindigar sun kuma fasa wani gidan yari a garin Wallam, inda fursunoni 62 suka tsere.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba