An janye jami'an tsaron Tambuwal

Hakkin mallakar hoto mohammed ibrahim
Image caption Tambuwal tare da wasu gwamnonin APC

An janye jami'an tsaron da ke kula da lafiyar Shugaban Majalisar wakilan Nigeria, Aminu Tambuwal kwanaki biyu bayan da ya koma jam'iyyar adawa ta APC.

Wani na hannun daman Tambuwal ya tabbatar wa BBC cewar tun a daren Laraba, fadar shugaban kasar ta ba da umunin janye 'yan sanda da jami'an tsaron farin-kaya da ke kare shugaban majalisar.

Wata sanarwa da kakakin 'yan sandan Nigeria ya fitar, ta ce Sufeto Janar ne ya bada umurnin janye jami'an tsaron Tambuwal saboda ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Sanarwar da Emmanuel Ojukwu ya sanya wa hannu ta ce Sufeto Janar din ya yi amfani da tanadin kundin tsarin mulkin kasar wajen bada umurnin.

Sai dai bayanai sun nuna cewar a ranar Laraba Mr Jonathan ya tattauna da jiga-jigan jam'iyyar PDP da wasu kusoshin gwamnati kan sauya shekar Tambuwal zuwa APC.

A ranar Laraba, Tambuwal ya halarci taron APC a Abuja inda kafofin yada labarai suka ambato shi yana cewar za su kawar da jam'iyyar PDP daga mulki a shekara ta 2015.