Blaise Campore ya yi jawabi ga 'yan kasar

'Yan Burkina Faso suna zanga-zanga Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Burkina Faso suna zanga-zanga

Shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Campaore ya yi jawabi ga al'ummar kasar kwana daya bayan da tashin hankali ya barke, lamarin da ya sa rundunar sojin kasar tace ta rusa gwamnatinsa.

A jawabin da ya yi ta wani gidan talabiji mai zaman kansa, shugaban ya ce, ya gane bukatar mutanen kasar daga irin zanga zangar da suka gudanar.

Ya kuma yi kara da cewa zai sauka daga shugabancin kasar nan da watanni 12.

To sai dai bangaren 'yan adawa da masu zanga zangar sun ce bukatarsu ita ce Shugaba Campaore ya ajiye mukaminsa ba tare da ba ta lokaci ba.

Karin bayani