Taba shafin Internet na wata kasa a'a - China

Babban Jami;in China mai kula da Internet Hakkin mallakar hoto Xinhua
Image caption Babban Jami;in China mai kula da Internet

Darakta mai sa ido kan huddar internet a kasar China ya amsa cewar ba za a iya shiga wasu shafukka na kasashen waje ba, amma dai ya musanta cewar an rufe su.

Lu Wei, wanda ke jagorantar Ofishin watsa labarai game da harkokin Internet ya kuma ce sashen na sa yana shirin karfafa matakai na sa ido kan harkoki na mu'amalla da internet.

Ba dai iya shiga shafukka na Twitter da Facebook da New Times a kasar China.

Tun farkon wannan watan ne aka toshe kafar shiga sashen Turanci na BBC.

Mr Lu din dai yana amsa tambayoyi ne a taron manema labarai dangane da taron kasashen duniya kan batutuwan harkar internet da za a gudanar a lardin Zhejian.

Da wani dan jarida ya tambaye shi ko me yasa aka rufe shafukka kamar na Facebook ? Mr Lu ya maida amsa da cewar, 2ban taba shiga wadannan shafukkan ba, don haka ba ni da masaniya kan ko an soke su ne. To, amma a yanayin da aka ka sa shiga wasu shafukkan, ina ganin hakan tana iya yiwuwa.

Yace,"ba mu taba rufe shafin wata kasar waje ba. Shafin ku yana kasar ku, to, ta yaya za a yi aje can a rufe su.

Sai dai kuma Mr Lu ya kara da cewar, a yayinda China take haba-haba da jama'a, za ta kuma iya zaben wanda zai je kasar ta, ya zama bakon ta.

Yace, "ba zan iya canza ka ba, to amma ina da karfin da zan iya zaben aminnai na", "ina fata dukkan mutanen da suka je China su zamo aminnai ne na kwarai."

Mr Lu ya kara da cewa matakan da sashen sa ke dauka, don bayar da kariya ne ga harkokin tsaro na kasar China da masu mu'amalla ko amfana da ita.

Karin bayani