Mubi: 'Yan gudun hijra sun shiga mawuyacin hali

Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yin kaurar ya hada har da mata da kanana yara

Dubban mutanen da suka bar gidajensu a garin Mubi sakamakon harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a Jihar Adamawa sun ce sun shiga mawuyacin hali.

A ranar larabar da ta gabata ne aka kai hare haren a garin na Mubi lamarin da ya sa mutane da dama suka fice daga garin domin kaucewa rikicin.

A Wata hira da wakilinmu Ishaq Khalid ya yi da wasu 'yan gudun hijra, ''yan gudun hijrar sun bayyana mai cewa batun abinci na daga cikin matsalolin da mutane ke fuskanta, musamman wadanda ke kan hanyar tafiya.

"Mun zo wani gari wanda ake ce masa Kasuwar Dare, sai yara suka fara kuka wai za su ci tuwo sai na siyo mana danyen dankali muka dukanmu muka ci." In ji wani dake ya fice daga garin Mubi tare da iyalansa.

Wannan hari na Mubi shine hari na baya bayan nan da 'yan kungiyar Boko Haram din suka kai ya kuma faru ne yayin da gwamnatin Najeriya ke ikrarin ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan kungiyar ta Boko Haram.