Boko Haram: Nigeria na bukatar daukin gaggawa

Alhaji Atiku Abubakar Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Alhaji Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Atiku Abubakar ya nemi kasashen duniya da su taimaka wa Nigeria don shawo kan matsalar tabarbarewar tsaro da kasar ke fuskanta.

A wani taron manema labarai a Abuja, tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana takaicinsa dangane da irin mawuyacin halin da dubban mutane a shiyyar arewa-maso-gabashin Najeriyar ke ciki, sakamakon hare haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa.

Alhaji Atiku Abubakar wanda wasu 'yan Majalisar dattawa da suka fito daga yankin arewa maso gabashin kasar suka rufa masa baya a wajen taron ya ce matukar ba a tashi tsaye ba, mayakan kungiyar Boko Haram ka iya mamaye daukacin kasar baki daya.

Don haka ya bukaci yan Najeriya da su nemi gwamnati da ta kara yin hobbasa don shawo kan matsalar ta Boko Haram a Najeriya.

Ya ce, idan kuma gwamnatin ba za ta iya ba, to kuwa ya kamata ta san inda dare yayi mata.