Kungiyar IS na ci gaba da kisan kare dangi a Iraqi

Mayakan IS na shirin kisan kare dangi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan IS na shirin kisan kare dangi

Kafofin kabilu da na hukuma a Iraqi sun ce mayaka masu da'awar kafa daular musulunci, IS, sun ci gaba da kisan kare dangi da suke yi kullum na 'yan wata kabila, 'yan Sunni, wadanda ke fada da su, a lardin Anbar.

Kafofin sun ce mayankan IS, sun jera sama da mutane talatin, 'yan kabilar Al Bu Nimr, da suka hada da mata da kananan yara suka harbe su.

Tun ranar Alhamis da ta wuce, akalla 'yan kabilar 200 ne mayakan IS, suka harbe bayan da suka kama garinsu da sauran garuruwan da ke kusa da su.

'yan kabilar sun ce, an rutsa mutanensu da dama, a can, kuma sun dora alhakin halin da suka shiga akan gwamnatin Iraqi saboda rashin kawo musu dauki.