Sojoji na nazarin bidiyon Boko Haram

Hakkin mallakar hoto reuters

Ma'aikatar tsaro ta Najeriya ta ce ta na nazarin sabon faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar.

A cikin bidiyon shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya musunta ikirarin da gwamnatin ta yi na cewa sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da kungiyar.

Ya kuma ce sun Musuluntar da 'yan matan Chibok da suka sace, sun kuma aurar dasu.

To amma a sanarwar da darektan yada labarai na hedikwatar tsaro, Majo-Janar Chris Olukolade, ta fitar dazu a Abuja, ma'aikatar tsaron Najeriyar ta ce tana nazarin faifain bidiyo, kuma za ta bayyana matsayinta kan batun a nan gaba.

Haka kuma ta ce tana tura karin dakaru da kayan yaki domin kwato wuraren da wadanda ta kira 'yan ta'adda suka kwace.

Karin bayani