Zida ya zama sabon shugaban Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto Getty

Rundunar sojin Burkina Faso ta ce ta amince da nadin sabon shugaban kasar, bayan rudanin da aka samu bayan korar shugaba Blaise Compaore.

Sojojin sun bada sanarwar cewa yanzu suna goyon bayan Laftanar Kanar Isaac Zida ne a matsayin sabon shugaban kasar.

Shugaban sojin kasar ne Janar Honore Traore ya sanya hannu a sanarwar.

Da farko dai Janar Traore ya yi shelar kansa a matsayin shugaban kasa, to amma sai masu zanga-zanga suka ki amincewa dashi, domin suna yi masa ganin matsayin wanda ke kud-da-kud da tsohon shugaba Compaore.

Ranar Juma'a da dare ne, Laftanar Kanar Zida na rundunar tsaron fadar shugaban kasa, ya bayyana a tashar telabijin ta kasar, ya na mai bayyana cewa ya karbi jagorancin kasar.

Ya ce: ''Yayinda muke jiran daidaitar al'amurra daga jam'iyyun siyasa da kungiyoyin fararen hula, a yau na karbi jagorancin duk wasu al'amurra da suka shafi gwamnatin rikon-kwarya da mika mulki hannun farar hula."

A ranar Juma'ar ne dai shugaba Compaore ya yi murabus bayan da yunkurin sauya fasalin tsarin mulkin kasar da zai bashi damar tsawaita wa'adin mulkinsa ya haifar da zanga-zanga a kasar.

Mista Compaore ya tsere zuwa kasar Ivory Coast, inda 'yan kasar Burkina Fason da dama ke zaune.

Mista Compaore babban aminin shugaban kasar Ivory Coast ne, Alassane Ouattara.

Karin bayani