'Mutane fiye da 15,000 na marawa kungiyar IS baya'

Image caption Ana ci gaba da fafatawa da mayakan IS

Wani sabon rahoto da majalisar dinkin duniya ta fitar ya nuna cewar fiye da mutane dubu sha biyar ne sukai tattaki zuwa kasashen Syria da Iraqi domin marawa masu tada kayar baya na kungiyar IS baya.

Rahoton da aka mikawa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniyar ya ce mutanen da ke wannan tattaki sun fito ne daga kasashe fiye da tamanin, wadanda a baya ba su taba fuskantar tada kayar baya daga mayakan IS ba.

Rahoton ya kuma ce hakan hadari ne ga Tarayyar turai da Asia da kuma Afurka.

Haka kuma rahoton ya gano yadda masu tada kayar bayan suke samun karin sabbin hanyoyin hada bama-bamai, kuma duk da banbancin da ke tsakaninsu shugabannin kungiyar Al-Qaeda da na IS su na gudanar da ayyukansu kusan iri guda.