Soji sun tarwatsa zanga-zanga a Wagadugu

Hakkin mallakar hoto AFP

Sojoji a Burkina Faso sun yi harbe-harbe ta sama don tarwatsa masu zanga-zanga a hedikwatar tashar telabijin ta kasar da ke Wagadugu, babban birnin kasar.

Rahotanni sun ce hakan ya faru ne jim kadan bayan isowar jagorar 'yan adawa, Sara Sereme, da wasu daga cikin magoya bayanta.

Jam'iyyun adawa sun bukaci gwamnatin rikon-kwarya ta farar hula ta karbi ragamar shugabancin kasar har ya zuwa lokacin da za'a gudanar da sabon zaben shugaban kasa.

Wani daga cikin masu zanga-zangar, Amadou Yamiro, ya dora laifin rikicin kan dakarun fadar shugaban kasar.

Ya ce: ''Da safiyar yau muka fito, saboda har yanzu muna cikin zaman rashin tabbas, har yanzu ba mu da shugaba a kasarmu."

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a birnin, Mohamed Ibn Chambas, ya yi gargadin yiwuwar sa wa kasar takukumi, muddin sojoji suka rike ragamar mulkin kasar.

Karin bayani