AU: Za a tattauna rikicin Burkina Faso

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kungiyar Tarayyar Afirka ka iya sanyawa Burkina Faso takunkumi idan sojoji suka ki bada mulki

Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce zata kira taron kwamitin tsaronta domin tattauna rikicin siyasar Kasar Burkina faso a ranar Litinin.

Rundunar sojin kasar Burkina Faso ta yi alkawarin kafa wata gwamnatin hadin kan kasa domin tsara mika mulki, bayan wani bore da 'yan kasar suka yi da ya tilastawa Shugaban Kasar mafi jimawa akan mulki, Blaise Compaore sauka daga kujerarsa a makon da ya gabata.

Sojoji sun yi harbi a babban birnin Kasar na Ouagagougou a ranar Lahadi domin tarwatsa masu zanga- zanga wadanda suka taru a wajen shedikwatar tashar yada labaran kasar.

Jam'iyyun adawa na kiran da a kafa wata gwamnatin farar hula wacce zata gudanar da mulki har zuwa lokacin da za a yi zaben Shugaban Kasa

Wani manzon kungiyar Tarayyar Turai a birnin Mohammed ibn Chambas ya yi gargadin yiwuwar sanyawa kasar takunkumi idan har sojojin suka ki bada mulki