Ebola na ci gaba da baraza a Saliyo

Jami'an lafiya na aiki akan gawar mai cutar Ebola Hakkin mallakar hoto ap
Image caption Wanke gawar mai cutar Ebola dai na barazana ga karuwar yaduwar cutar a kasar Saliyo.

Kungiyar bada agaji ta kasashen duniya ta yi gargadin cewa yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola na karuwa a kasar Saliyo daya daga cikin kasashen yammacin Afurka da cutar ta fi kamari a ciki.

Babban jami'in hukumar tallafawa kananan yara ta Save The Children yace mutanen yankin na cikin firgici matuka.

Mr Forsyth wanda ke ziyara kasar Saliyo ya shaidawa BBC cewa har yanzu ba akai ga shawo kan matsalar yaduwar cutar ba.

Sai dai yace taimakon hukumar ya fara kawo wasu sauye-sauye, ya kuma yi kiran da a sake wayar da kan al'uma game da cutar Ebola, musamman ta fuskar wayar da kan mutane game da illar da ke tattare da wanke gawar mai cutar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar cutar Ebola ta hallaka fiye da mutane 5,000, ya yin da wasu fiye da 10,000 suka kamu da ita.