An halaka mutane fiye da 300 a Iraqi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana ci gaba da fafatawa da mayakan IS a Iraqi

Jami'ai a Iraqi sun ce mayakan IS masu da'awar kafa daular musulunci sun halaka 'yan wata kabilar 'yan sunni fiye da 300 dake yakar su a lardin Anbar.

Ma'aikatar kare hakkin dan adam ta Iraqi tace an gano gawawwakin mutane fiye da hamsin da suka hada da mata da kuma kananan yara a cikin wata rijiya.

Majiyoyi daga kabilar Al-Bu Nimr sun ruwaito cewa ana karkashe musu mambobi tun daga ranar Alhamis.

A wani waje a Iraqi kuma, wata mota makare da bom dake nufin kai hari kan masu ziyarar ibada 'yan shi'a ta halaka mutane 12 a Bagdad.

Ana tsammanin kai irin wadannan hare- hare gabanin bikin ranar Ashura ta 'yan shi'a