Za a yi taron jami'an tsaro a Ukraine

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Poroshenko ya ce gwamnatinsa ba za ta amince da sakamakon zaben ba.

Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine ya kira taron manyan jami'an tsaro na gaggawa, bayan zaben da 'yan aware magoya bayan Rasha suka yi a gabashin kasar .

A wata hira da aka watsa agidan talabijin Mr Poroshenko gwamnatinsa ba za ta taba amincewa da zaben ad aka yi a yankunan Donetsk da Luhansk, wanda ya kira da na kokarin tada zaune tsaye ne.

Ya kuma kara da cewa zai nemi a soke wata doka da ta bawa yankunan da yan tawaye ke rike da su, damar ayyana cin gashin kansu, wanda da a aka amince da shi a matsayin wani shiri na zaman lafiya. Za kuma a tattauna kan wannan batu ya yin taron jami'an tsaro a yau talata.

Tun da fari kakakin hukumar tsaron Ukraine Andriy Lysenko yace zaben ba halattace ne ba, ya kuma ce hukumar tsaron kasar bata amince da zaben da aka gudanar a yankin Donetsk da Luhanks da masu tada kayar baya suka yi ba,su na nanata cewar hukumar tsaro ta fara gudanar da bincike kan zaben.