An daure Warg saboda yin kutse cikin kwamfitoci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption An kuma taba samun Warg na Pirate Bay da laifin satar fasaha

An yankewa daya daga cikin mutanen da suka kirkiro da shafin internet na Pirate Bay Gottfrid Warg hukuncin daurin shekaru 3 da rabi a gidan yari saboda samunsa da laifin yin kuste cikin kwamfitoci da kuma sauke wasu fayil fayil ba tare da izni ba.

Wata kotu a Denmark ce ta same shi da laifin yin kutse cikin kwamfitoci mallakar katafaren kamfanin fasaha na CSC.

Shi da wanda ake yanke musu hukuncin tare, sun sauke fayil fayil na 'yan sanda daga kwamfitocin.

Masu gabatar da kara sun ce wannan shi ne kutse mafi girma ya zuwa yanzu.

Jim kadan bayan an bada sanarwar yanke hukuncin, lawyoyin dake kare Mr Warg sun ce zasu daukaka kara.

Lawyoyin dake kare shi sun ce kodayake an yi wannan kutse ne bayan an yi amfani da wata kwamfita mallakar Warg, amma sai dai ba shi ne ya yi amfani da kwamfitar wajen sauke fayil fayil din ba.

Sai dai sun ce wani mutum ne daban ya yi amfani da kwamfitar Warg wajen kaddamar da kutsen.

Warg dai ya ki ya bayyana sunan daya mutumin.

Wannan hukunci da kotun ta yanke shi ne na uku da aka yankewa Warg a cikin shekaru biyar dinda suka gabata.

An tusa keyarsa daga Cambodia a watan Satumbar shekarar 2013 zuwa Sweden inda ya yi zaman gidan yari bayan samunsa da laifin satar fasaha.

An kuma taba yanke masa hukuncin zaman gidan yarin shekaru biyu a gidan yarin Sweden saboda yin kutse cikin kwamfitocin bankuna.

Amma daga baya an rage wannan hukunci zuwa shekara guda bayan da ya daukaka kara.