An yi kutse a Kwamfitocin Fadar white House

Fadar White House Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an Amurka ba su bayyana ko an saci wasu bayanai a Kwamfitocin ba.

Masu satar bayanai sun yi kutse a Kwamfitocin fadar White House a Amurka.

An dai yi kutse a kwamfitar daya daga cikin ofishin shugaban kasa kamar yadda jaridar Whashington post ta rawaito.

Hukumomin Amurka na gudanar da bincike kan wannan kutse, wanda abokan huldar Amurka ne suka sanar da jami'an kasar.

Haka kuma jami'an fadar White House sun yi amanna da cewar akwai sa hannun na gida a lamarin, sai dai ba su bayyana ko an saci wasu bayanai ba.

A wata sanarwa da aka aikewa kamfanin dillancin labarai na AFP, fadar White House ta ce wasu daga cikin abubuwan da ke cikin Kwamfitocin sun samu illa.

Wani jami'in fadar da bai so a bayyana sunan sa ba ya shaidawa jaridar Washington Post cewa a dalilin barazanar da suke fuskanta a baya-bayan nan sun gano wasu abubuwa a cikin Kwamfitocin.