Shugaban Guinea ya soki AU kan Ebola

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde Hakkin mallakar hoto
Image caption Mr Conde ya yi marhabin da taimakon da ake samu, dan rage yaduwar cutar Ebola.

Shugaban kasar Guinea ya soki sauran kasashen yammacin Afurka kan yin shakulatun bangaro da kasarsa akan barkewar cutar Ebola.

Shugaba Alpha Conde ya shaidawa BBC cewa gwiwarsa ta sare, akan matakin da kasashen da ke makotaka da Guinea da mambobin kungiyar tarayyar Afurka suka dauka na kulle iyakokin kasasahen.

Mr Conde ya yi marhabin da karin taimakon da ake samu na kasashen duniya dan magance yaduwar Cutar Ebolar, sai dai ya yi gargadin cewar wannan bala'i ya durkusar da tattalin arzikin kasar ta Guinea.