Burkina Faso: Ghana za ta kwashe 'yan kasar ta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin siyasar Kasar Burkina Faso ya sa Ghana ta fara tunanin kwashe mutanen ta daga kasar

Gwmnatin Ghana ta ce za ta kwashe 'yan kasar ta da ke zaune a kasar Burkina Faso idan harkokin tsaro suka kara tabarbarewa a Kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen Ghanan ta umarci ofishin jakadancin Kasar dake Burkina Faso da ya tuntubi shugabannin al'ummar Ghanan dake kasar domin sanin halin da suke ciki, da kuma yadda za'a tattara su domin kwashe su idan ta kama.

Hakan kuma na zuwa ne bayan da kwamitin tsaro da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afrika, ya yi kira da a mika mulki ga farar hula a Burkina Fason cikin sati biyu.

Sojin da suka karbi mulki a Burkina Faso bayan da shugaban kasar, Blaise Campore, ya sauka daga mulki ranar Juma'a, sun ce, farar hula ne zai jagoranci gwamnatin riko da za a kafa.

Mutumin da sojojin suka zaba, ya zama jagoran kasar na wucin gadi, Laftana Kanar Isaac Zida, ya sheda wa jakadun kasashen waje, cewa, dukkanin bangarori ne za su zabi mutumin da za a nada shugaban rikon.