Potiskum: El-Zakzaky ya zargi sojoji

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A duk shekara 'yan shi'a ke bukin ashura

Kungiyar 'yan uwa Musulmi ta mabiya akidar Shi'a a Nigeria ta yi Allah-wa-dai da harin bam din da aka kai wa wani jerin-gwano na 'ya'yan kungiyar a Potiskum yayin da suke gudanar da bikin ashura a kasa baki daya.

Shugaban kungiyar, Sheikh Ibrahim El-zakzaky ya ce da ma kungiyar tana sane game da shirin kaddamar musu da irin wannan hari a taronsu.

Sheikh El-Zakzaky, yana zargi sojin Nigeria da kai wannan harin a kan 'yan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi.

Yace "Bam din ya hallaka mutane 15 sannan kuma sojoji da bindiga suka harbe mutane biyar."

Kungiyar dai na cewa 'ya'yanta ba su takali kowa ba yayin wannan muzaharar.