Mata 'yan gudun hijira hudu sun haihu a Yola

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin Boko Haram ya raba dubban mutane da muhallansu

Hukumar agajin gaggawa a Nigeria, NEMA ta ce kawo mata hudu sun haihu a sansannin 'yan gudun-hijira da ke Yola cikin mutanen da suka tsere daga Mubi.

Shugaban NEMA a shiyyar arewa maso gabashin Nigeria, Alhaji Muhammad Kanar wanda ya shaida wa BBC hakan, ya ce har yanzu ana samun kwararar 'yan gudun-hijirar zuwa babban birnin jihar Adamawa watau Yola.

Tun bayan da 'yan Boko Haram suka kwace iko da garin Mubi, 'yan gudun-hijira sama da dubu goma ne suka yi tururuwa zuwa Yola.

'Yan gudun-hijirar sun koka game da rashin abinci da kuma muhalli ingantace.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta ce tana iyakacin kokarinta wajen taimakawa 'yan gudun hijirar wajen ba su kayan abinci da na kwanciya.