Gwamnonin APC sun kaurace wa taron kasa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Gwamna Kwankwaso da Aminu Tambuwal

Shugaban majalisar wakilan Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal da duka gwamnonin APC sun kaurace wa taron majalisar kasa da aka yi ranar Talata.

Su ma tsofaffin shugabannin kasa kamar Janar Muhammadu Buhari da Ibrahim Babangida da kuma Abdulsalam Abubakar ba su halarci taron majalisar kasar ba, wanda shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta.

Amma tsofaffin shugabanni kamar su Cif Olusegun Obasanjo da Janar Yakubu Gowon da Alhaji Shehu Shagari da kuma Cif Ernest Shonekan sun samu halarci taron.

Su ma galibin gwamnonin PDP sun halarci zaman wanda aka yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

A lokacin taron, majalisar ta amince da Sulaiman Abba a matsayin Sufeto Janar na 'yan sandan kasar.