An kai hari a kamfanin siminti na Ashaka

Image caption Jihar Gombe na makwabta da jihar Yobe inda 'yan Boko Haram ke iko da garuruwa da dama

Rahotanni daga garin Gombe sun ce 'yan Boko Haram sun kai hari a kamfanin siminti na Ashaka.

Wani mazaunin garin ya ce 'yan Boko Haram din suna cikin kamfanin sun kuma lalata abubuwa da dama a cikinsa da wajensa, haka kuma an gan su da wasu motocin kamfanin makare da wasu buhuna.

Kazalika mazauna garin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye, sun ce suna jin karar harbe-harbe a cikin garin na Bajoga, musamman ma a yankin da ofishin 'yan sanda yake.

Kafin kai farmaki Ashakan, 'yan Boko Haram sun kai hari a garin Nafada na jihar, ranar Talatar, inda suka kona caji ofis na 'yan sanda da banki da kuma ofishin PDP da ke garin.

Kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da hare-haren.

A makon da ya gabata ne 'yan Boko Haram suka kai hari a wata tashar mota a Gombe inda mutane da dama suka rasu.