'Yan Boko Haram sun yanke hannun wasu a Mubi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A makon jiya ne garin Mubi ya fada hannun 'yan Boko Haram

Rahotanni daga garin Mubi na jihar Adamawa a Nigeria na cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram sun aiwatar da hukuncin kisa a yayin da suka yanke hannayen wasu da suka samu da laifin sata.

A makon da ya gabata ne garin Mubi ya fada hannun kungiyar Boko Haram.

Kawo yanzu dai babu wani tashin hankali ko fada, amma 'yan kungiyar na ci gaba da kona coci coci da ke cikin garin na Mubi.

A yanzu haka an fara bude kantuna da kasuwanni, yayin da jama'a ke shiga su kuma fita daga cikin birnin ba tare da wata matsala ba.

Haka nan kuma jama'a sun fara ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum a karkashin ikon 'yan kungiyar Boko Haram.