Shafin 'yan luwadi ya samu kudi a China

'Yan Luwadi a China Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan Luwadi a China

Wani shafin sada zumunta na haduwar 'yan luwadi a China ya samu jari na dola miliyan 30 daga rukunin wasu masu hannu da shuni.

Shafin na sada zumunta mai suna Blued wanda wani kamfani mai suna DanLan ya kirkiro a shekara ta 2012 ya yi ikirarin samun mutane miliyan 15 masu amfani da shi.

Kafofin watsa labarai na Tech Asia sun ce yawancin masu amfani da shafin sun fito ne daga manyan birane ukku da suka hada da Beijing da Shanghai da Guangzhou.

Kafin shekara ta 1997 Luwadi ko madigo a China haramun ne, kuma ana kallonsu a mmatsayin wani abu na rashin hankali, zuwa shekara 2001 ne tabi'ar ta zamo jiki.

Xiaofeng Wang - wani mai sharhi a cibiyar bincike ta Forrester ya fada a wani rahoto cewar shafin na apps ya fi samun karbuwa a China saboda hanyar sadarwa ta internet ta wayar salula ba ta da sauri.

Sai dai kuma yayinda 'yan Luwadin da Madigo ke amfani da wannan sarari ba tare da wani boye-boye ba, wani shafin na neman abokan soyayya Maza da Mata yana da kimanin mutane miliyan 52 dake amfani da shi - shafin na masu neman jinsi irin na su a China, ba shi da farin jini sosai.

Rupert Angus-amann wani marubuci a Internet ya bayyana cewa 'yan Luwadi da Madigo a Beijing a mafi yawan lokutta ba su cika bayyana kansu ba.

Yace, "da wuya, ka samu wanda ke da bukatar a fallasa shi."

Kididdiga ta hukuma ta nuna cewar a tsarin Iyalai na China a kan samu Yara Maza 118 ko kowanne adadi na 'yan Mata 100.

Mr Angus-Mann ya kara da cewa, manufar China ta kyale Iyalai su haifi da daya tun a shekarar 1979 na nufin yawancin yaran da suke da shekaru 29 da kasa da haka, ba su da 'yan uwa.

Karin bayani