Shin me yasa sojoji suka tsere daga Mubi?

Harin 'yan Boko Haram
Image caption Harin 'yan Boko Haram

A Nijeriya, ana ci gaba da samun bayanai game da yadda mayakan kungiyar Boko Haram suka kwace wasu garuruwa a jihar Adamawa.

Garin Mubi dai shi ne gari na baya-bayan nan a Jihar da 'yan Boko Haram din suka kwace a makon jiya...

...kuma wasu mazauna garin sun ce sojojin kasar sun tsere bayan da suka kasa tunkarar mayakan kungiyar ta Boko Haram.

Daya daga cikin sojojin Nigeria da suka tserewa mayakan Boko Haram ya bayyana dalilan cewa, ba su iya fafatawa da 'yan Boko Haram din ba saboda rashin makamai, shi yasa suka tsere.

Karin bayani