'Yan gudun hijirar Nigeria 12,000 na Nijar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Boko haram na ci gaba da kai hare-hare a Najeriya, lamarin da ke kara yawan 'yan gudun hijira

A jamhuriyar Nijar rahotanni na cewa yawan 'yan gudun hijirar Najeriya na dada karuwa a yankin jihar Difa mai iyaka da Borno.

Wasu alkaluma da kungiyoyin agaji suka wallafa a baya-bayan nan na nuna cewa sama da 'yan gudun hijirar 12,000 ne suke samu mafaka a cikin karamar hukumar Boso, kuma adadinsu na karuwa kowace rana.

Masu gudun hijirar dai sun gudo ne daga yankunan jahar Borno sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar boko haram ke kai wa garuruwansu.

Wasu dubban 'yan gudun hijirar ne ke samun mafaka a kasar Kamaru, yayin da wasu dubbai kuma suke gudun hijirar a wasu jihohin da ke cikin Najeriya.