Masu cutar HIV na zanga-zanga a Nigeria

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Masu boren sun ce Amurka ta fara janye tallafin da take musu shi yasa suke neman gwamnati ta taimaka

A Nigeria, an shiga rana ta biyu da masu dauke da cutar HIV ko SIDA ke wata zanga-zanga a Abuja bisa korafin halin-ko-in-kula daga hukumomi.

Masu zanga-zangar sun tare kofar shiga hukumar da ke yaki da cutar, NACA, inda suka sha alwashin ci gaba da zaman dirshan har na tsawon kwana 25, muddin ba a biya musu bukatunsu ba.

Sakataren kungiyar, Victor Olaore, ya ce a yanzu sai sun biya kudi kafin a yi musu gwaji a asibiti, kana kuma babu magungunan cutar a asibitoci kamar da.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar suna zargin hukumar da ke yaki da cutar ta HIV da ci da guminsu, inda suka ce suna kashe kudin da ake warewa na yaki da cutar ta wata hanya daban.

Jami'an hukumar dai sun bayyana zanga-zangar a matsayin wani yunkuri na kawo musu tarnaki a ayyukansu.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba