Ashura: An kashe mutane biyar a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sarki Abdullah na Saudiyya

Ma'aikatar harkokin cikin gida a Saudi Arabia ta ce ta damke mutane shida bisa zargin hannu a harbe-harben da ya janyo rasuwar mutane biyar tare da jikkata wasu mutane tara.

'Yan bindiga masu shigar burtu sun bude wuta kan wasu Musulmai masu bikin Ashura al-Dalwah ranar Litinin.

Kakakin 'yan sanda ya ce uku daga cikin maharan sun yi amfani da manyan bindigogi da kananan a lokacin da suka yi harbin.

Ma'aikatar ta ce an damke mutanen ne bayan wani samame a yankin Riyadh da ke lardin Ah-Ahsa da ke birnin al-Khobar a gudundumar gabashin kasar.