Sauyin dimokradiyya ya ja baya a Burma

Aung San Suu Kyi Hakkin mallakar hoto Getty

Fitacciyar 'yar rajin kare dimokradiyyar nan ta Burma, kuma wadda ta samu kyautar zaman lafiya ta Nobel, Aung San Suu Kyi, ta ce sauye-sauyen da ake yi a kasar sun tsaya cik a cikin shekaru biyun da suka wuce.

Da take magana a wani taron manema labarai ta gargadi shugabannin duniya da ka da su saki jiki, su kyautata zaton cewa shirin kasar na sauyi daga mulkin soji zuwa na farar hula na tafiya yadda ya kamata.

Ta ce ana bukatar karin hadin kai domin cim ma sauye-sauyen da ake son samu a kundin tsarin mulkin kasar.

Ta ce, ''A ce mun yi aniyar sauya tsarin mulkin ta hanyar majalisar dokoki. Wannan shi ne matsayin jamiyyarmu ta NLD.''

Aung San Suu Kyi, ta yi kalaman ne kafin ziyarar da Shugaba Barack Obama zai kai kasar, a mako mai zuwa.

Myanmar, wadda kuma ake kira Burma ta fara aiwatar da sauye-sauyen siyasa da na tattalin arziki shekaru uku da suka gabata, abin da ya sa har aka cire mata wasu takunkumin da aka sanya mata.