Tsagaita wuta: Nigeria ta yi amai ta lashe

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Gwamnatin ta ce 'yan jarida ne ba su fahimci abin da ake nufi ba

Da alama gwamnatin Nigeria ta yi amai ta lashe a kan batun ayyana tsagaita bude wuta da 'yan kungiyar Boko Haram.

Gwamnan jihar Akwa Ibom Godswill Akpabio, ya shaida wa manema labarai cewa ba a cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta da 'yan Boko Haram ba.

Gwamna Akpabio ya bayyana hakan ne bayan taron majalisar kasa da aka yi a Abuja a ranar Talata, inda ya ce mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Sambo Dasuki, ne ya ce ba a cimma yarjejeniya da 'yan Boko Haram din ba.

Sai dai kalaman na gwamna Akpabio sun ci karo da sanarwar babban hafsan tsaron Nigeria Air cif Marshal, Alex Bade, wanda ya fito karara ya ce an cimma tsagaita bude wuta da 'yan Boko Haram a cikin watan Oktoba.

Shi ma dai shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau a wani faifan bidyon da ya fitar ya ce ba wata tattaunawa da suke yi da gwamnatin Nigeria.